Gaskiya Mai Ɗaci – Kalaman Buhari Ga Matasan Najeriya


Tun jiya ake kace nace akan kalaman shugaba Muhd Buhari na cewar “Da yawa daga matasan Nijeriya malalata ne”.

Hakika wannan furucin ya jawo muhawara amma a ra’ayina, da yawa daga cikin masu sukar zancen sun kasu kashi kashi, cikin su akwai malalatan da aka taba kuma suke son mai da martani, wadanda lalaci ya hana su neman ainihin bidiyon su saurara domin gane abin da aka fada, wannan kashin sun dogara ga abin da suka gani a Facebook ko kuma a radiyo mai jini.

Haka kuma akwai bangaren ‘yan adawa wadanda ke jiran Buhari ya kwafsa su yi maye fake da agana, irin wadannan sune ma suke saurin jirkita maganar domin ta yi musu dadin yadawa. Ga kashin farko na malalatan da ba za su saurari ainihin maganar ba.

Amma ni a ra’ayina maganar Buhari gaskiya ce, domin hakika da yawa daga matasan Nijeriya Malalata ne,(karfa ku manta da yawa daga ciki ba duk gaba daya ba) wasu daga ciki lalaci ya hana su karatu, wasu kuma sun yi karatun amma kuma sai karatun nasu ya sangarta su, suka kasa komai sai neman aiki me maiko, na ofis, ko kuma jiran arzikin dare daya ko kuma wata ma’ida daga sama.

Irin wadannan matasan ne cima zaune, idan suka rasa abinci sai su zagi shugabanni, alhalin ga ‘yan uwansu can a kasuwannin singa da Kwari suna dako, su kuwa sun fi karfin haka.

To dan Allah idan ba a kira wadannan malalata ba wanne suna ne ya dace da su?

Yawancin mutanen mu ba ma son gaskiya musamman mai daci, mun fi son a gaya mana abin da zai yi mana dadi koda ba mai yiwuwa ba ne.

Dan haka wadannan Kalamai na PMB, duk wanda ka ga yana jan ido akan su to yana cikin rukunin mutane uku.1. Malalaci ne wanda aka yi magana akansa ya tsargu. 2, mai adawa da Buhari wanda ya jirkita maganar tare da yi mata fassarar son zuciya domin cimma bukatar sa. Kashi na 3 kuma sune wadanda suka fada tarkon kaso na 2, wadanda ba su ji ainihin maganar ba amma suka kasa nema su ji, suka dogara da karatun kaso na 2.

Allah ka ba mu ikon yi wa junan mu adalci koda kuwa za mu fada tarkon mai zargi da zagi. Allah ya tsare mu da imaninmu.

You may also like