
Asalin hoton, …
Miliyoyin mutane a ciki da wajen nahiyar Afirka sun kalli wasu bidiyoyi da ke nuna yadda wasu duwatsu ke samar da lantarki.
Ɗaya daga cikin bidiyoyin ya nuna yadda wutar ke tartsasti yayin da aka haɗa duwatsun biyu, inda aka rubuta kalaman da ke cewa ”An samu duwatsun lantarki a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo”.
Wannan bidiyo ya yaɗu kamar wutar daji a lokacin da hamshaƙin ɗan kasuwar Afirkan nan Daniel Marven ya wallafa shi a shafinsa mai mabiya dubu 800 tare da rubuta kalaman: ”Ƙarin matsaloli na tunkaro mu, ina tausaya wa nahiyata Afirka”
Wani mai amfani da shafin Tuwita, ya yi tsokaci a kan bidiyon da Marven ya wallafa, ta hanyar wallafa wani bidiyo da ke nuna wani mutum riƙe da kwan lantarki ɗaure da wayoyi guda biyu inda kwan lantarkin ke kawo hasken wuta da zarar ya jona wayoyin a jikin wani ƙaramin dutse da ke hannunsa.
Sa’o’i bayan nan ne kuma Marven ya sake wallafa wannan bidiyo a shafin nasa, inda fiye da mutum miliyan ɗaya suka kalle shi.
Fitaccen shafin Tuwitan nan mai suna ‘Africa Archives’ ya sake wallafa duka bidiyoyin biyu, inda ɗaya daga cikin bidiyoyin aka kalle shi sau kusan miliyan 35.
To sai dai babu tabbas game gaskiyar lamarin duwatsun.
Bincike ya nuna cewa bidiyon farko da Marven ya wallafa, an fara wallafa shi a shafin Facebook na Jami’ar Mohamed na ɗaya, da ke Oujda a Morocco.
Inda aka rubuta kalmar ”Lithium!!?” ba tare da ƙarin bayani ba.
BBC ta tuntuɓi Jami’ar, to sai dai har yanzu babu martani daga gare ta.
To amma abu mafi muhimmanci shi ne shin da gaske ne duwatsun da aka nuna a bidiyon za su iya riƙe ko samar da lantarki?
Dakta Ikenna Okonkwa malami a sashen koyar da ilimin ma’adinai na jami’ar Najeriya ya ce ”ba zai yiwu ba”.
Ya ce “Duwatsun sun yi kama da ma’adinin zinc ko dalma, don haka ba su da ƙarfin ma’adinin da zai samar da lantarki”.
Za su iya riƙe wutar da ire-iren ma’adinai irinsa ke da ita, to amma ba ta da ƙarfin da za ta haska kwan lantarki”, in ji Dakta Okonkwo.
Don haka a ganinsa wannan bidiyo kawai wani ”siddabaru ne”.