George Weah Ya Gayyaci Arsene Wenger Bikin Rantsar Dashi



Sabon Shugaban Kasar Laberiya wanda kuma ya taba rike kambu dan kwallon duniya, Sanata Gearge Weah ya gayyaci mai horas da ‘yan wasan Kulub din ‘ Arsenel”, Mista Arsene Wenger wajen bikin rantsar da shi a matsayin Shugaban kasa.

Mista Arsene Wenger, wanda ya taba zama Manajan Shugaban Laberiyan a lokacin yana bugawa Kulub din, Monaco a shekarar 1988, ya nuna cewa rayuwar Gearge Weah tana kunshe da tarihi kama tun da ya zo fagen kwallon kafa ta yadda bai san kowa ba amma har ya kai ga rike kambun dan kwallon da ya yi fice a duniya sannan kuma a yau, shi ne Shugaban kasar Laberiya

You may also like