
Asalin hoton, Getty Images
Hauhawar farashin ƙasar Ghana a watan Nuwamba ya ƙaru zuwa kashi 50.3 daga kashi 40.3 a watan da ya gabace shi, cewar alƙaluman baya-bayan nan da Hukumar Ƙididdigar Ghana ta fitar.
Wannan ce hauhawar farashi mafi girma a shekaru gommai kuma ana alaƙanta hakan da tsadar farashin gidaje da ruwan sha da lantarki da iskar gas da sauran makamashi, waɗanda hauhawar farashinsu ya kai kashi 79.1.
A ranar Talata, Asusun ba da Lamuni na Duniya da Ghana suka amince da wata yarjejeniyar farko kan wani shirin ceto tattalin arziƙin ƙasar na dala biliyan uku amma da sharaɗin amincewar hukumar gudanarwar asusun matuƙar ƙasar ta cimma dukkan tanade-tanaden da aka gindaya mata.
Shirin zai taimaka wajen dawo da daidaito a harkokin ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, ya kuma tabbatar da ɗorewar harkokin lamuni.
Amma sai gwamnati ta sake fasalin harkokin takardun lamunin ƙasar zuwa wani mataki mai ɗorewa don ta cancanci samun bashin IMF.
Sai dai masu takardun lamuni a cikin gida sun ƙi amincewa da shawarar gwamnati ta musanya dala biliyan goma da rabi na takardun lamuni da wasu sabbi saboda ba su yarda da sabbin sharuɗɗa ba.
Tun a makon jiya, takardar cedin Ghana take ta farfaɗowa idan an kwatanta da dalar Amurka bayan ta yi asarar fiye da rabi na darajarta a bana.
Sai dai ba a ga wani canji ba a farashin kayan masarufi da ake shigarwa ƙasar daga ƙetare. Ƙasar mai arziƙin koko da zinare ta Afirka ta Yamma na faɗi tashin shawo kan rikicin tattalin arziƙi mafi muni a tsawon wani zamani, wanda har ya haddasa jerin zanga-zanga a kan titunan babban birnin ƙasar.