Shugaban Ghana ya sanar da amincewar kasarsa kan aikewa da sojoji zuwa kasar Senegal domin shiga cikin sahun rundunar hadin gwiwa ta kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da zasu yi amfani da karfi wajen kawar da shugaba Yahaya Jamme’i daga kan karagar mulkin kasarsa.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo- Addo ya bada umurnin aikewa da sojojin kasar 205 zuwa kasar Senegal domin shiga cikin rundunar hadin gwiwa ta kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yammacin Arika ta ECOWAS da zasu yi amfani da karfi wajen kawar da shugaba Yahaya Jamme’i daga kan karagar shugabancin Gambiya matukar yaki amincewa da shirin mika ragamar shugabancin kasar ga zababben shugaba Adama Barrow.
Tun a cikin daren jiya Laraba ce rundunar sojin Nigeriya 200 tare da rakiyar jiragen yaki suka kama hanyar kasar Senegal domin tsoma baki a dambaruwar siyasar kasar ta Gambiya.
Tun a cikin daren jiya Laraba ne wa’adin da aka dibawa shugaba Yahaya Jamme’i na ya amince ya mika ragamar shugabancin kasar ga zababben shugaba Adama Barrow cikin ruwan sanyi ko kuma ya fuskanci amfani da karfin tuwo daga rundunar sojin kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS.