Ghana za ta fara rigakafin maleriya | Labarai | DWHukumomin kasar Ghana sun amince a fara amfani da sabuwar allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro ko kuma maleriya a kasar. Amincewa amfani da rigakafin wacce jami’ar Oxford da ke Birtaniya ta sarrafa shi ne karo na farko da wata kasa a duniya ta yi domin kariya daga maleriya.

Jami’an da suka hada rigakafin sun ce gwajin da suka yi a kan kananan yara na kasar Burkina Faso ya nuna cewa allurar na da karfin kaso 80 cikin 100 na bayar da kariya daga kamuwa da cutar cizon sauron.

Sanarwar da jami’ar Oxford din ta fitar ta ce kawo yanzu rigakafin za ta takaita ga kananan yaran kasar Ghana da ke a tsakanin watanni 5 zuwa 36, rukunin mutanen da suka fi hatsarin mutuwa daga wannan cuta.

 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like