Gidan Dariya: Aradu Ban Yi Sanyi Ba


 

 

 

Wani Bafulatani ne ya shigo birni, yana cikin tafiya sai fitsari ya kama shi. Ai kuwa sai ya koma gefen hanya ya kama fitsarinsa.

Ashe ‘yan sanda sun kafe sambodi dauke da dokar hana fitsari a wurin. Da ganinsa sai ‘yan sanda suka nufo shi suna cewa mun kama ka da laifin karya doka. Kana fitsari a inda hukuma ta hana.

Bafulataninka da jin haka ko tsayawa ya gama daure wandonsa bai yi ba sai ya zuba a guje. Ai kuwa ‘yan sanda suka bi shi da gudu.

Yana zuwa wajen wani mai gyaran firji sai ya bude wani firji ya shiga ciki ya rufe. Ashe daya daga cikin ‘yan sandan ya gan shi, yana zuwa sai ya kwankwasa firji ya ce: “Waye a ciki?” Sai danfulani ya ce: “Kunun aya ne da zobo.” dan sanda ya ce: “Fito mu sha.” Sai danfulani ya ce: “Aradu ban yi sanyi ba.”

 

 

 

 

cc:alummata

You may also like