Gidan rediyo ya maka gwamnatin Jihar Bauchi a kotu


Tun bayan da gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da sanarwar bukatar muhallinta wanda aka mallaka wa gidan rediyon Ray Power Fm dake Bauchi da gidan talabijin na AIT, mahukuntan gidan rediyon sun bayyana cewar korar da gwamnatin ke shirin musu ya saba wa doka.
Ita kuma gwamnatin jihar tana ikirarin cewar ba da wa’adin mako biyu ga gidan rediyon hanya ce da take kokarin inganta kafafen sadarwarta na cikin gida.

Bayan gwamnatin ta ba da makonni biyu ga gidan rediyon da ya tattara nasa ya nasa ya fice mata daga muhalli, kana ya dawo wa gwamnatin jihar da na’urrorinsu da suka hada da Tiransimita da kuma Ereas, sai gidan rediyon garzaya kotu.

Kwamishinan Hukumar Tsara Birane, Abubakar Tararari Ali ya fitar da sanarwar.

A zantawar da suka yi da wakilinmun shugaban gidan rediyo na Ray Power, Alhaji Yusuf Bala ya bayyana cewa tsohuwar gwamnatin jihar ce ta ba su wannan muhallin da ake takaddama a kai tsakaninsu da gwamnati mai ci.

“Tsohuwar gwamnati ta ba mu wannan wajen, mun kuma cika dukkanin sharadin mallaka. Babu yanda za a yi wata gwamnati ta mallaka maka waje idan wata gwamati kuma ta zo ta janye wancan damar, amma gwamnati tana da ikon yin hakan.”

Ya kuma yi zargin cewa lamarin na da nasaba da goyon bayan da gidan rediyon yake samu daga al’umar jihar ta Bauchi.

Ya yi kira ga gwamnatin ta tabbatar da ta bi doka kan , domin a cewarsa wa’adin makwanni biyu sun yi kadan.

“A doka, babu yadda za a yi a ce maka a sati biyu mutum ya tattara ya-na-shi-ya-na-shi ya bace. Ya kamata ne a ce a karin farko a baiwa mutum wata shida, idan ba ka samu damar tashi ba a kara maka, ba a kore ka nan take ba”.

Ya kuma bayyana cewar zasu bi duk wata hayar da doka ta shimfida domin samun adalcim

A tattaunawar da ‘yan jaridu sukai da mai baiwa gwamnan Jihar Bauchi shawara kan dukkanin aiyuka, Air Kwamando Baba Gamawa (ritaya) wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin kwato kaddarorin da gwamnatin baya ta raba su ba bisa ka’ida ba. Inda ya bayyana korar da suka yi wa gidan rediyon bai da alaka da siyasa kamar yanda wasu ke zargi.

“Kwamitinmu ya gano an mallaka wa gidan rediyon izini ne ba bisa ka’ida ba hade da daukan kayan gwamnati na na’urori a basu. Don haka ne gwamnati ta bukaci amsar kayanta domin inganta kafafen sadarwarta na cikin gida. Sannan kaya ne na al’umman jihar Bauchi, dole ne gwamnati ta tabbatar ta nema musu hakkinsu a wajen kowaye”.

Sai dai kuma, a yayin da kungiyar ‘yan jarida, reshen Bauchi ta ziyarci gwamnan jihar don sulhunta lamarin, gwamnan jihar ya ce za su sake duba matakin korar da nufin sassautawa.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da tafka shari’a, inda kotun ta dakatar da wannan umurnin korar na tsawon mako biyu.

Ana dai ganin gidan rediyon tare da talabijin na AIT da ke jihar sun shahara wajen baiwa ‘yan adawa damar caccakar lamirin gwamnatin jihar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like