Gidauniyar Ganduje Ta Tallafawa Wata Mata Da Mijinta Ya Sake Ta Ya Bar Ta Da Yara Saboda Halon Babu 



A ranar Talatar da ta gabata ne Gidauniyar Raya Addinin Musulunci ta Ganduje ta tallafawa Maryam dake zaune a Unguwar Dorayi a karamar hukumar Gwale. Ita dai Maryam, mijinta ya sake ta har ta kai ma ba su da abinda za su ci su sha balle tufafi.
A ranar Lahadi da ta gabata ne Gidauniyar Ganduje Foundation ta yi shelar rabawa jama’ar shiyar Kano ta Tsakiya magani kyauta inda wannnan Mata ta kai yaranta guda uku wadanda ba sa iya yin komai saidai a yi musu. Inda bayan duba lafiyarsu Likitoci suka tabbatar da kamuwar yunwa a jikin wadannan yaran. Inda nan take aka sada su da shugabannin da suke kula da wannan Gidauniyar suka ji abinda yake faruwa .
A ranar Talata da ta gabata ne Uwargidan Gwamnan Jihar Kano, ato Dr Hafsatu Umar Abdullahi Ganduje wadda Hajiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta wakilce ta suuka sauka a gidan wannan mata dake Unguwar Dorayi domin kai mata tallafin kayan abinci da suka hada da shinkafa, masara, gero, gari da sauran abinci mai gina jiki da kuma kudi. 
Daga bisani kuma Gwamna Ganduje ya umarci Kwamishinar Mata da walwalar Jama’a da ta je ita ma domin duba yadda Gwamnati za ta taimakawa wannan matar domin samo yadda za ta dogara da kanta ta kula da Yaranta da karatunsu.

You may also like