Gidauniyar Kwankwasiya ta tallafawa matasa 3007 da jari


Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dake wakiltar mazabar Kano t Tsakiya ya tallafawa matasa 3007 da suka fito daga mazabarsa.

An zabo wadanda suka ci gajiyar shirin daga kananan hukumomi 15 dake mazabar.

A jawabinsa na bude taro shugaban kungiyar Kwankwasiya, Barrister Aminu Dala ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin da su tabbatar sun karbi katin zaben su domin su kafa gwamnati a shekarar 2019.

Ana sa jawabin shugaban kwamitin tsare-tsare na kungiyar, Danburan Abubakar Nuhu, ya ce matasa sune kashin bayan kowanne irin cigaba saboda haka akwai bukatar a taimaka musu su zamo masu dogaro da kai.

Nuhu ya tabbatar da cewa idan kwankwasiya ta kafa gwamnati to za a samar da wasu karin shirye-shirye na tallafawa mutane domin rage zaman banza a tsakanin matasa.

Darakta Janar na Gidauniyar Kwankwasiya, Alhaji Sanusi Surajo Kwankwaso ya yabawa sanatan kan gudunmwar inda ya ce kudin da aka bayar na tallafin zai taimakawa wadanda aka bawa.

You may also like