Gidauniyar Kwankwasiyya ta tsohon gwamnan jihar Kano,Rabi’u Musa Kwankwaso, ta bawa mata 100 jari a jihar Yobe domin su zama masu dogaro da kai.
Dakta Surajo Kwankwaso, wanda ya wakilci tsohon gwamnan ya ce tallafin wani bangare ne na gangamin rage talauci da suke a kasa baki daya.
Ya ce shirin ɗorawa ne kan nasararorin da aka samu na tallafawa mata lokacin da sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake mulkin Kano.
“A wancan lokacin mun zabo mata marasa galihu daga kananan hukumomi 44 inda muka rika basu tallafin ₦10,000 a karshen kowane wata labarin mai daɗin ji ne domin dukkaninsu sun nuna kwazo,’ ya ce.
Kwankwaso ya ce wadanda suka ci gajiyar shirin an zabo su ne cikin tsanaki daga kananan hukumomin jahar 17 ta yin la’akari da rashin galihunsu.
Haka kuma gidauniyar ta bayar da tallafin takalman kwallo, kwallaye, da kuma rigunan kwallo ga kungiyoyin wasan kwallon kafa na matasa dake fadin jihar.