Gidauniyar Muhammad Indimi Ta Raba Kayan Abinci Na Naira Miliyan 100 Ga Yan Gudun Hijira Dake Maiduguri 


Gidauniyar Muhammad Indimi, ta raba kayan abinci da suka kai naira miliyan dari da kuma tallafin kudi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu wadanda ke zaune a sansanin yan gudun hijira dake Maiduguri. 

Mai magana da yawun gidauniyar, Sam Umukoro, ya bayyana haka inda yace tallafin  wani bangare ne na kokarin gidauniyar na rage wahalhalun da yan gudun hijirar suke fama dasu. 

Yace mutane 28,000 ne suka amfana da kayan tallafin a sansanonin yan gudun hijira dake Maiduguri , a karo na biyu da gidauniyar take bada tallafin ga mutanen da suke warwarewa daga rikicin Boko Haram. 

Da take jawabi yayin raban kayan tallafin babbar darakta a gidauniyar, Amina Indimi tace sai da suka duba abubuwan da yan gudun hijirar suke da bukata a shekarar 2016, kafin su shigo su fara bada tallafi don taimakawa kokarin gwamna Kashim shettima na tallafawa yan gudun hijirar. 

” A wannan shekarar ta 2016, mutane 10,000 ne suka karbi jakar abinci da kudi a yankin arewa maso gabas kadai,asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya yayi kiyasin cewa yara 200 zasu iya mutuwa saboda yunwa. A wannan shekara mun ga bukatar mu kara abinda da ake rabawa zuwa buhu daya na kayan abinci daban-daban, tare da rabawa kai tsaye ga mata domin iyalansu. Haka kuma a wannan karon muna sa ran rabawa mutane 28,000 da suka hada da mata, maza da kuma yara. Zamu cigaba da shiga cikin kokarin da ake na sake gina yankin arewa maso gabas. ” tace. 

Wata mace, Hamsatu mai yaya takwas , daya daga cikin mazauna sansanin yan gudun hijira na Madinatu tace tallafin gidauniyar na wannan shekarar yazo a lokacin da yadace. 

You may also like