Gini ya rufta wa mutane a Faransa | Labarai | DWAn yi nasarar samun gawarwakin mutane biyu daga baraguzan wani ginin bene da wasu ababen fashewa suka ruguza shi a yankin Marseille na kasar Faransa. Hukumomi sun ce kawo safiyar Litinin din nan sun kara kaimi domin gano sauran wasu mutane shida da ba a ji duriyarsu tun bayan da ginin ya rufta ba.

Samun gawarwakin mutane biyun na zuwa ne kimanin sa’o’i 24 bayan da fashewar wani abu mai kama da bam ta yi sanadiyyar rushewar ginin mai bene hawa hudu a wannan gari da ke kusa da teku. Kawo yanzu ba a gano musabbabin tarwatsewar ababen fashewar ba, amma wasu na cewa fashewar tukunyar gas ce ta haddasa al’amarin.

 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like