Girke-girken Ramadan
Girke-girken Ramadan: gashin tarwaɗa da karfasa a zamanance
Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.
A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, da ke nuna mana yadda ake gasa tarwaɗa da karfasa, don masu azumi.
Deejerh_delicatedishes_ng kamar yadda aka fi sanin ta a shafukan zumunta, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake gasa tarwaɗa da karfasa a zamanance.
Girki ne da mai azumi, ba zai so ya wuce shi ba, idan an sha ruwa!