Latsa lasifikar da ke sama domin kallon bidiyon
Girke-girken Ramadan: Yadda ake dafa chicken doughnut
Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.
A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, da ke nuna mana yadda ake dafa chicken doughnut, don masu azumi.
Rahama Sanusi Mato wadda aka fi sani da Mato favourite disheses a shafin Instagram, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake dafa chicken doughnut.
Girki ne da mai azumi, ba zai so ya wuce shi ba, idan an sha ruwa!