Girke-girken Ramadan: Yadda ake haɗa miyar ayayo
Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.
A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, da ke nuna mana yadda ake haɗa miyar ayayo ta zamani.
Maryam Tafida wadda aka fi sani da Tafida’s Glamour a shafin Instagram, mai girki ce gwana kuma ta nuna mana yadda ake yin wannan miya ta ayayo a zamanance.
Girki ne da mai azumi, ba zai so ya wuce shi ba, idan an sha ruwa!