
Asalin hoton, HADLEE RENJITH
Padayappa fitacce sunan ne a Kudancin Jihar Kerala na Jihar Indiya.
An san giwar dajin mai manyan kunnuwa da babban hanci ne da shakuwa da mutane.
Yanayin shakuwar Padayappa da mutane dadadden lamari ne da ya kwashe gomman shekaru a Jihar Kerala.
Mutanen garin Munnar, wato kusa da mazaunin Padayappa suna kiran giwar, “mai saukin sha’ani” wanda bai taba cutar da kowa ba, duk da cewar yakan dauke musu abinci a gida ko gona a cikin dare.
Sunan giwar ya samo asali ne daga fitaccen fim din nan Padayappa na 1999-Fim din da aka yi a kan cin amana da mutuncin iyali- wanda fitaccen jarumi, Rajinikanth ya taka rawa a ciki.
Haka kuma Padayappa ya zama wani abin sha’awa, inda mutane da dame ke tururuwar zuwa daukar hoto da shi.
Amma a ‘yan watannin nan, giwar wanda ake tunanin ya haura shekara 50, ya fara canja salo, inda ya fara rigima.
Mutanen garin sun ce Padayappa da a da can ke shigowa gari ya yi ta yawonsa, yanzu ya fara zama abin tsoro a tsakanin mutane.
A Janairu, wani rahoto ya nuna cewa ya fasa gilashin wata babbar mota, sannan ya gudu zuwa wani gonar wake ya yi barna.
Wannan barnar na cikin irinta da yawa da Padayappa ya yi da suke nuna ya fara rigima, wanda ya jawo aka fara shiga damuwa.
Wasu sun alakanta rigimar Padayappa da girma- lokacin da sinadaran haihuwa na namijin giwa kan karu, wanda ke sanya shi ya zama rigimamme
Asalin hoton, HADLEE RENJITH
Sai dai masana na ganin kusancin mutane da mazaunin Padayappa ne ya kawo matsalar.
“Ko giwayen da suka kai lokacin da sinadaran haihuwar suka taru, ba su cika zama rigamammu ba sai an tabo su,” inji Dokta PS Easa, wanda mamba na Kungiyar Kwararrun Likitocin Giwaye na Asiya.
Ya kara da cewa, “Padayappa na bukatar nisa da mutane, inda zai wataya sosai.
” Akwai bukatar a ba mazaunin giwaye kariya sosai,”
A baya, mutuwar giwa mai ciki bayan ta ci ayaba ya tayar kura. Wata mata tana so ta ceci giwayen da aka azabtar a Indiya.
An sha samun rahotannin rikici tsakanin mutane da dabbobi a Indiya, wanda bai rasa nasaba da rashin dazuka, wanda ke tursasa dabbobin shigowa cikin mutane domin neman abinci da mafaka.
A Kerala, wasu batattun giwaye da suka rabu da garkensu, sun kashe mutum 105 a tsakanin 2018 zuwa 2022.
A Janairu, bayan malaman dajin sun kama giwa daya a yankin Palakkad, sun ga alamar harbin bindigar baushe sama da 12.
Mutanen gari sun ce giwar ta fitini kauyensu na watanni, har suka yi zargin ta kashe wani mutum.
Wadanfa suka san Padayappa sun bayyana shi a matsayin daban da sauran giwaye.
Lalita Mani, wadda ke zaune a wani gari a kusa da Munnar ta ce Padayappa ya zo gidanta akalla sau uku ya ci ayaba da kuka.
Ta ce akwai lokacin da ya tuge bishiyoyin ayaba guda 10 a gonarta, sannan ya tsaya ya cinye ayabar a tsanake kafin ya tafi.
Duk da haka, Mani ba ta da komai ga Padayappa, sai dai kauna.
“Yana zuwa ne a duk lokacin da yake jin yunwa. Ba ya cutar da kowa,” inji ta.
Ana ganin Padayappa yana yawo ne a tsakanin dajin Munnar, duk da cewa yakan zagaya wasu wuraren.
Hadlee Remjith, wanda mai daukar hoton dabbobin daji ne kuma wanda ya dade yana bibiyar Padayappa tun a 2014, ya bayyana shi da babbar dabba, sannan a cewarsa, “Kahonsa na hagu ya fi na dama girma kadan.”
Mista Renjith yana gani giwar akalla sau biyu a wata. “Ina daukarsa daga nesa ne. Ba ya damuwa da ni, amma da alama yana tsayawa domin a dauke shi hoton,” inji shi, sannan ya kara da cewa Padayappa shi ne giwa ‘mafi shakuwa’ da mutane da ya taba gani.
Labarai a kan barnar Padayappa da shakuwarsa da mutane sun sa ya kara haskawa.
Idan yana wucewa, mutanen gari suna tsayawa domin ya wuve. Masu yawan bude ido suna zuwa su dauki hoto da shi. Haka masu shaguna sun ce ba su cika damuwa ba idan ya musu barna a shago domin hakan yana kawo musu kwastoma.
“Padayappa ya zama jakadanmu,” inji Vinod Vattekkag, Shugaban Gidauniyar Showcase Munnar, wadda ke fafutikar habaka wuraren shakatawa a yankin.
Asalin hoton, HADLEE RENJITH
Masu yawon shakatawa kan tsaya su ɗauki hoto da giwar
Wannan ne ya sa sauyin halayyar Padayappa ya ba mutane mamaki.
A Disamba, an ce Padayappa ya ture wasu babura guda biyu lokacin da masu ababen hawa suka tare masa hanya. Mutanen da ke kan baburan suna kokarin daukar hoton giwar ne.
A Afrilu, ya bi wata motar bas mai dauke da kusan fasinja 50, ya fasa mata gilashi.
Sai dai masoyansa suna ganin yana rigima ne saboda mutane da suke “tsokalarsa”
Mista Renjith ya tuno wani abu da ya faru a bara, lokacin da Padayappa yake kokarin tsallake titi, wani direban mota sai ya yi yunkurin gaggawar wucewa maimakon ya jira.
“Padayappa bai bugi motar ba, sai ya tura hancinsa cikin motar, wanda hakan ya sa gilashin motar ya fashe,” inji mai daukar hoton, wanda ya kara da cewa nan take kuma ya yi gaba abinsa.
Asalin hoton, HADLEE RENJITH
Padayappa a cikin sauran giwaye
Suresh Palraj, wanda yake aiki a gonaki a Munnar, ya ce direbobin kananan da manyan motoci suna yawan tsokalar giwan ne.
A Disamba, malaman daji sun shigar da karar wani mutum wanda ya yi yunkurin firgita Padayappa domin ya bar gonar kayan shayinsa ta hanyar bugun hancinsa.
Haka kuma masana sun ce yadda masu shakatawa suke rububin zuwa yankin bayan kullen Covid yana cikin abun da ke bata ran Padayappa.
“Babu wani abun mamaki a yanayin halayyar Padayappa. Dukkan giwayen daji suna fusata idan aka kusance su domin daukar hoto,” inji masanin dabbobin daji, James Zachariah, wanda ya bibiyi Padayappa na gomman shekaru.
“Suna kai farmaki ne saboda suna tsoron za a kawo musu farmaki. Amma hakan ba yana nufin dole su farmaki mutum ba,” inji shi, sannan ya kara da cewa yana tunanin cewa yawancin labarin Padayappa da ake bayarwa “ana kara gishiri” a ciki.
Tun lokacin da labarin Padayappa ya fara yawo a Indiya, jaridu da dama suna ta bin labarin.
Wata jaridar da ta rubuta ra’ayinta game da shi, ta tunatar da makarantanta cewa Padayappa “na bukatar kulawa da girmamawa.”