GOBARA DAGA TEKU: Yadda Kamfanin Atiku Ya Maka Gwamnatin Najeriya a Kotu


Mummunar rashin jituwar nan wadda Premium Times Hausa ta kawo rahoton cewa ta faru tsakanin kamfanin Intels, mallakar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Gwamnatin Najeriya a karkashin Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa, yanzu abin ya kara muni har sun garzaya kotu.

Intels ya zargi gwamnati da karya yarjejeniya, inda hakan ya ce wata kullalliya ce domin yi wa kamfanin sa zagon-kasa. Tuni da Premium Times Hausa ta samu kwafen takardun bayanan shari’ar da za a tabka a kotu.

A cikin watan Mayu, hukumar tashoshin jiragen ruwa ta shaida wa kamfanonin da ke hada-hada a tashoshin sakon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, cewa an karkasa ayyukan tashoshin zuwa matakai uku: Na manyan jirage, jirage masu safarar kwantinoni da kuma jirage masu karakaina.

Sannan kuma an sake tsari a tashar jiragen ruwa ta Onne wadda kamfanin Intels mallakar Atiku ne ke kula da hada-hada a tashar.

A takaice kenan gwamnati za ta bude tashar a matsayin mai karbar kowane irin jirgin safara, maimakon jiragen Lodi da jigilar fetur da gas kadai.

Wannan tasha ta Onne ita ce tasha mafi muhimmanci wajen jada-hadar fetur da gas a Najeriya, kuma a cikin ta ake cutar da kashi 65 bisa 100 na abin da ake fitarwa kasashen waje, a cewar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa.

Amincewar da Shugaban Kasa ya yi, ta na kuma dauke da cewa “kowane mai shigo da kaya a cikin kasar nan, ya na da ‘yancin zabar tashar da zai rika sauke kayan da ya kawo daga waje.”

A takaice dai wannan bayani na nufin an karya lagos kaka-gidan da kamfanin Intels na Atiku ya yi kenan.

Nan da nan sai Intel’s ya garzaya Babbar Kotun Tatayya ta Abuja, inda ya kalubalanci wannan tsari. A cikin sammacen kotu, Intels ya na karar hukumar tashoshin jiragen ruwa, ministan shari’a, da kuma uwa-uba gwamnatin tarayya wacce dama ita ce a farkon wacce aka maka a kotun.

Takardar karar wadda aka gabatar wa kotun tun a ranar 4 Ga Yuni, ta nina cewa sabon tsarin da da aka shigo da shi ya karya yarjejeniyar da gwamnati ta kulla da Intels a ranar 25 Ga Oktoba, 2005.

A wannan rana ce dai aka amince wa Intels kula da hada-hada a tashoshin Warri biyu, wato tsohuwa da sabuwar tasha, tashar Kalaba da kuma ta Onne A da Onne B.

Takardar yarjejeniyar ta Nina cewa an kulla amincewar yin harkokin ne har tsawon shekaru 25.

A kan haka ne sai Intels ya shigar da kara a yanzu, inda ya ke neman kotu da ta dakatar da gwamnati daga ci gaba da gudanar da kowace irin hada-hada ko bayar da duk wani umarnin jiragen ruwa su yi harkokin da suka shiga hurumin yarjejeniyar da tun farko aka kulla da kamfanin Intels a tashoshi biyar da aka lissafa a sama.

Babban lauyan Intels, Dominic Onwuchekwa, ya gabatar wa kotu da hujjojin cewa kamfanin su ya zuba jari da kuma kadara akalla na dala bilyan 10 ta hanyar gudanar da ayyuka daban-daban a tashoshin biyar.

Duk kokarin jin ta bakin hukumar tashoshin jiragen ruwa ya ci tura, domin jami’an hulda da ‘yan jarida, Nduonofit Effiong bai dauki wayar kiran da aka yi masa ba.

Kamfanin Intels dai Atiku ne da wani Baturen Italiya mai suna Gabriel Volpi suka kafa shi, a farkon shekarun 1980.

A lokacin da Atiku ya fito takarar zaben 2015, ya bayyana cewa Intels ne babban karfin arzikin sa a duniya, ku shi ne kamfanin da ya fi tinkaho da shi a cikin sauran kamfanonin da ya mallaka.

Baya ga wannan sabani na tashoshin jiragen ruwa, wani rikici da Intels ke tafkawa da gwamnatin tarayya shi ne batun zuba kudaden harajin da Intels din ke tara wa gwamnati a tashoshin ruwa a cikin asusun bai-daya tilo na gwamnati, wato TSA. Wannan rikicin kuwa Premium Times Hausa ta kawo rahoton sa a makonnin da suka gabata.

You may also like