Gobara ta ƙona wata katafariyar gonar shinkafa a jihar Bauchi


Gobara ta kona wata gonar shinkafa mai girman gaske a da ake shirin fara girbinta a Liman Katagum  a jihar Bauchi

Gonar mallakin Nasiru Muhammad Darakta a Kamfanin Futlink West Africa Limited da kuma Auwal Muhammad.

Da yake magana da ƴan jaridu mai kula da gonar,Ahmad Muhammad yace har  yanzu basu san musabbabin gobarar ba.

A cewarsa gobarar ta kwashe sa’o’i biyu tana ci kuma ta kone shinkafa ta miliyoyin naira.

“Wutar ta kama ganga-ganga, ta dade tana ci da taimakon busassun ganyaryaki da kuma iska dake kaɗai  dai-dai lokacin da aka lura da ita tuni ta lalata ko ina dake gonar.Wannan gonar tana samar da aiki ga matasa sama da 1000 a jihar. Saboda haka muna kira ga masu ruwa da tsaki da su kawowa mutanen da suka zuba jarinsu ɗauki waɗanda suka rasa hanyar cin abincinsu.” Ya ce.

Ana sa ɓangare daya daga cikin mutanen da suka mallaki gonar Nasiru Muhammad ya bayyana lamarin matsayin wani abu marar daɗi  inda yace ya yi asarar daruruwan miliyoyi a gobarar.

You may also like