Gobara ta Ci Kasuwar Karasuwa A Jihar Yobe


A yammacin jiya Litinin 12/03/2019, Allah ya jarrabi kasuwar Karasuwa Girun Guna, dake karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe da gobara wanda ta yi sanadiyya asarar dukiyoyin al’umma gami da kone shaguna da rumbuna.

Shaidar gani da ido ya bayyana cewa akalla kimanin rumufuna da shaguna sama hamsin ne suka kone. Amma cikin ikon Allah da kuma taimakon al’umma an yi nasarar kashe wannan wuta.

Kawo yanzu dai ba a san menene ya yi sanadiyar aukuwar wannan gobara ba.

You may also like