Gobara ta kashe mutane 27 a Indiya | Labarai | DWGobara ta halaka mutane 27 wasu da dama sun mutu a wani benen kasuwanci mai hawa hudu a New Delhi babban binrin kasar Indiya, hukumomi sun ceto mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran Indiya Press Trust ya ce mutane 12 sun kone a gobarar, an kuma kwashe wasu 50 daga benen byan da jami’an kashe gobara suka shafe fiye da sa’o’i biyar suna kokarin shawo kan lamarin.

Yanzu haka dai ana ci gaba da neman sauran mutanen da suka makale a cikin ginin, sai dai kawo yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba. Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya bayyana kaduwarsa kan asarar rayuka daga gobarar. 

Irin wannan tashin gobarar dai ta zama ruwan dare a Indiya, inda ake zargin magina da saba dokokin gini da ka’idojin kariya.You may also like