
Asalin hoton, Olivier Klein
Mutum goma ne suka mutu, ciki har da kananan yara biyar, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gida a kusa da Lyon da ke Faransa, a cewar hukumomin karamar hukumar.
Wata sanarwa da hukumomi suka fitar ta ce wata “gobara mai dan girma” ta tashi a ginin mai hawa bakwai da ke unguwar Vaulx-en-Velin.
Mutum hudu na cikin mawuyacin hali yayin mutum goma suka ji kananan raunuka, cikinsu har da ma’aikatan kashe gobara guda biyu.
Ma’aikatan kashe gobara 170 ne suka yi ta fama har ta kai su ga kashe ta.
Olivier Klein, ministan birane da gidaje na lardin Borne, ya wallafa sako a shafinsa na Tuwita ranar Juma’a da safe inda ya ce: “Alkaluman mutanen da suka mutum sun jefa mu cikin tashin hankali.”
Ministan cikin gida, Gerard Darmanin, ya ce kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba kuma ya yaba wa ma’aikatan kashe gobara game da yadda suka kubutar da mutane “wadanda suka shiga mawuyacin hali”.
Ya kara da cewa kananan yaran da suka mutu ‘yan tsakanin shekara uku zuwa 15 ne.
Mr Darmanin ya ce ranar Juma’a za a soma gudanar da bincike game da abin da ya haddasa gobarar.