Gobara ta kona gidaje 36 da kuma tumaki,awaki 40 a Jigawa


Wata gobara da ta tashi a safiyar yau Litinin ta kone gidaje 36, rumbuna 46 ta kuma kashe awaki da tumaki 40a ƙauyen Abandari dake karamar hukumar Dutse ta jihar.

DSP Abdu Jinjiri mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar shine ya tabbatarwa da manema labarai haka a Dutse.

 Jinjiri yace wutar wacce ta fara da ƙarfe 5 na asubahin ranar Litinin a tunanin kona daji da ake yi ne ya haddasa tashin ta.

“Yau da misalin ƙarfe 5 na asuba an samu gobara a ƙauyen Abendari  dake ƙaramar Hukumar Dutse kuma gobarar ana tunanin ta samo asaline daga wutar daji.

“A sanadiyar haka, gidaje 36, rumbuna 46 dake dauke da kayayyakin abinci daban-daban da kuma awaki da tumaki 40 duka sun kone sun zama toka,”jinjiri ya ce.

Yace babu wanda ya mutu a gobarar amma tuni aka fara bincike kan lamarin.

You may also like