GOBARA TA KONE MUHIMMAN ABUBUWA A KWALEJIN ILIMI TA JIHAR ZAMFARA 



A daren ranar Asabar din da ta gabata 23 ga watan Disamban nan ne wata gobara ta lakume kayayyaki na miliyoyin naira a kwalejin koyar da aikin malanta mallakar jihar Zamfara. 

Gobarar dai ta tashi cikin daren Asabar din ne da misalin karfe 10 na dare a sashen koyar da nazarin harsuna a kwalejin.

Wani da lamarin ya faru kusa da shi ya shaida wa majiyar mu cewa, gobarar ta lalata sashen koyar da harsuna wato languages a turance da kuma wani bangare na koyar da aikin gona. 

Shugaban kwalejin, Alhaji Nasir Sarkin Fawa Mafara ya ce, babu asarar rayuka a sanadin gobarar, sai dai asarar muhimman bayanai na sashen sun salwanta.

You may also like