Mutane 2 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata sakamakon wuta da ta kama a asibitin koyarwa na jami’ar Bergmannsheil na kasar Jamus.
Sanarwar da aka fitar daga ofishin kashe gobara na Bochum ta ce, wutar da ta kama a dakin wani mara lafiya da ke hawa na 6 ta yadu cikin gaggawa a asbitin.
Sanarwar ta ce, ana ci gaba da kokarin kashe wutar inda ma’aikata sama da 200 ke gurin.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Arewacin Ren Raif Jaeger ya sanar da cewa, 6 daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.