Gobara Ta Lashe Motar ‘Yan Kasuwa Daga Kano Zuwa Zamfara A daren shekaranjiya Laraba ne, wata motar jigila makare da kayan ‘yan kasuwar karamar hukumar Kaura Namoda dake jihar Zamfara ta kama da wuta tare da konewa kurmus da duk kayan da take dauke da su, akan hanyar ta ta dawowa daga Kano zuwa zamfara. Akasarin kayan dake cikin motar kayan magani ne na milyoyin nairori. 

Wata majiya ta nunacewa motar dakon kayan ta saki hanya ne wanda a sanadiyar haka motar ta fadi ta kone da kayan dake ciki kurmus. 
Dama dai Allah ya albarkaci ‘yan garin Kaura Namoda da yawan kasuwanci wanda har ta kai aduk ranar Talata ta Allah suke cika motoci zuwa Kano domin sayo kayayyakin ciniki kala-kala. 
Shidai wannan lamari bako ne ga ‘yan kasuwar na garin Kaura Namoda domin kusan a ce wannan shine karo na biyu. 
Sai dai hadarin ya auku ba tare da rasa rayuwar kowa ba.
Sanarwa: Ba hoton motar bane

You may also like