Kayayyaki na miliyoyin naira ne suka ƙone bayan da wata gobara ta tashi da safiyar yau a sananniyar kasuwar nan ta sayar da magunguna dake Onitsha.
Gobarar wacce ta fara tashi da misalin ƙarfe 6 a layin da ake kira Redemption, an ce an samu nasarar shawo kanta sakamakon ɗauƙin gaggawa da jami’an kashe gobara dake babbar kasuwar Onitsha suka kawo da kuma wadanda ke kasuwar sayar da kayayyakin gini ta Ogidi.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa babu wanda ya rasa ransa a lamarin.
Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci kasuwar ya ga yan kasuwar suna duba irin asarar da suka yi a lokacin da suke ɗebe tarkacen kayan da gobarar ta kona.
Wani dan kasuwa da lamarin ya shafa, Uchenna Emeze ya bayyana gobarar a matsayin wata masifa mai muni inda yace ya rasa kuɗi ₦700,000 yayin da ya rasa kayayyaki na miliyan ₦15,000,000.