Gobe za’a Rufe Shirin Daukar Dalibai A Jami’o’i – JAMB 



Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta kasa ( JAMB) ta jaddada cewa a gobe Laraba ne wa’adin ba da guraben ilimi a jami’o’in kasar nan na kaakar karatun 2016/2017 zai cika inda ta kalubalanci jami’o’i kan su mutunta wannan wa’adi wajen dakatar da daukar dalibai.
Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin ne ya sanar da haka inda ya nuna cewa an tsawaita wa’adi da makonni biyu ga kwalejojin horas da malamai da na kimiyya da fasaha don su ci gaba da daukar dalibai. Ya kuma nemi jami’o’in kan su gabatar wa hukumar jerin sunayen daliban da suka dauka don hukumar ta tuntube su.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like