
Asalin hoton, GODWIN EMEFIELE/TWITTER
Rahotannin da ke kara-kaina a wasu kafafen yada labarai na cewa hukumar tsaron farin kaya na shirin kama gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.
Wata babbar kotu a Abuja babban birnin kasar ta yi watsi da bukatar DSS ta kamawa da tsare Mista Emefiele.
DSS na tuhumar Godwin da laifukan da suka shafi taimakawa ta’addanci, sai dai kotun ta ce hukumar ta koma ta samo ƙwararan hujjoji da shaidu kafin ta sake dawowa gabanta kan batun.
Abin da kotu ta ce game da batun Emefiele
Wani mai suna US Gambarawa shi ne ya shigar da karar a madadin hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar 7 ga watan Disambar 2022.
Tuhumar mai lamba FHC /ABJ/CS/2255/2022, ta nuna shari’ar tsakanin DSS da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.
DSS na zargin Godwin Emefiele, da tallafawa ta’addanci da kudade hakan ya sabawa doka ya kuma aikata laifi kan tattalin arziki.
Mai shari’a John Terhemba Tsoho da aka gabatar da karar gaban shi ya yi watsi da ita.
Ya ce DSS ba ta gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ta nuna gwamnan CBN din ya aikata laifin ba, sannan kamata ya yi ace shugaba Muhammadu Buhari ya san da batun.
Takardun tuhumar da kotun ta yi watsi da su, da sashen BBC Pigin ya gani, ya nuna alkalin babbar kotun ne ya dauki matakin.
A hukuncin da ya zartar, Alkalin ya yi bayani kan wasu bayanai da aka yi su a dunkule da ya bukaci a warware da yin bayani dalla-dalla, inda aka ambaci Godwin Emefiele ba tare da an fadi mukaminsa na Gwamnan babban bankin Najeriya ba.
Alkali Tsoho ya kara da cewa ”DSS ba su yi gamsasshen bayani kan ko wanda suke kara mai suna Godwin Emefiele gwamnann CBN ne ko kuma wani mutum mai irin sunansa na daban, don haka ana bukatar wannan bayani.
“Mutane za su yi mamaki da rudani ko wanda ake tuhumar Emefiele na CBN ne ko a’a, saboda ana magana ne fa a kan daya daga cikin babban jami’in gwamnatin tarayya.”
Mai Shari’a Tsoho, ya kuma kafe cewa kamata ya yi tuhumar da DSS suka gabatar ta samu rattaba hannun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tun da shi ne ya nada Emefiele mukamin.
”Lamarin ya yi kama da kotun na son fakewa da guzuma ne ta harbi karsana, ta hanyar amfani da kotun wajen lullube abin da suka aikata ba daidai ba da sun san ya sabawa doka kuma ba za a amince da shi ba.
“Wannan dalilin ne ya sanya ba mu amince da karar da suka shigar ba, har sai sun gabatar da kwakkwarar hujja sannan za mu saurare su, amma ayanzu kam mun yi watsi da batun,” in ji Alkali Tsoho.
Ana ikirarin amtsalar da Emefiele ke ciki na da alaka da sauya takardun Naira
Tun lokacin da Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da sabunta wasu daga cikin takardun naira, aka fara matsawa Mista Godwin Emefiele lamba.
Majalisar dattijan Najeriya ta nuna rashin amincewa da wasu daga cikin tsare-tsaren sabbin kudin, hakan ya biyo bayan bayanan Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmad da ta ce sam ba ta da masaniya kan batun.
Har wa yau, majalisar wakilai ma ta gayyaci gwamnan CBN domin amsa tambayoyi kan sabbin kudaden da kuma yadda zai shafi tattalin arzikin Najeriya.
A ranar Litinin wasu daga cikin lauyoyin kungiyar kare hakkin dan adam, da jam’iyyun adawa da kungiyoyin farar hula sun fantsama tituna zanga-zanga.
Masu boren karkashin gamayyar kungiyoyin farar hula, sun ce DSS ta maka Emiefele gaban kotu ne domin su bata masa suna.
Sun yi kiran Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Shari’a Abubakar Malami su shiga batun.
DSS ta ce batun kare tsaron kasa ake yi
DSS ta yi karin bayanin cewa tana bincike ne kan duk wani abu da ya shafi tsaron kasa. Kuma ayyukan da suke yi ya shafi ‘yan Najeriya ne baki daya.
Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya fitar da sanarwa a ciki yana cewa wasu mutane na yada farfaganda domin ɓata musu suna da aiki.
“Za mu ci gaba da aiki da bayyana sakamakon bincike ga ‘yan kasa ba tare da kunbiya-kunbiya ba, za mu sanar da wadanda lamarin ya shafa ba tare da boye-boye ba,” in ji sanarwar.
”Babu wata farfaganda da za ta yi tasiri a kanmu, ko wani abu da zai tsorata ni damu ba, ba bu wata barazana da za ta yi tasiri a kanmu.”