
Asalin hoton, Getty Images
Golan Kamaru Andrea Onana ya yi ritaya daga buga wa kasarsa wasa, makonni bayan rashin jituwa tsakaninsa da koci Rigobert Song.
Dangantakar mai tsaron ragar da koci Song ta yi muni, har ta kai Onana ya fada masa cewa kada a saka shi wasan da kasar ta yi da Serbia a Qatar 2022.
Hakan tasa aka sallame shi daga sansanin tawagar, kuma ba tare da bata lokaci ba ya baro Qatar.
Mai shekaru 26 ya fada ranar Juma’a cewa “Labarina da tawagar kwallon kafar Kamaru ya zo karshe.”
Dan wasan na Inter Milan ya kara da cewa “ Yan wasa na zuwa su tafi, sunaye suna dushewa, amma Kamaru tasha gaban duk wani dan wasa ko wani mutum.”
Onana ya fara buga wa tawagar Indomitable Lions wasa a shekarar 2016, kuma kawo yanzu ya buga mata wasa 34.
Kamaru ta gaza tsallake Rukuninta a gasar kofin duniya, inda ta kare a karkashin Brazil da Switzerland.