Goodluck Ne Ya Haifar Da Yaduwar Boko Haram – Osinbanjo


 

 

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya dora alhakin yaduwar ‘yan kungiyar Boko Haram a kan gazawar gwamnatin baya ta Goodluck Jonathan na samar da kayayyakin aiki ga sojoji

A yayin da yake jawabi a wajen yaye daliban makarantar sojoji ta NDA a jiya Alhamis a Kaduna ya bayyana cewa wannan gazawa ita ta haifar da rayuwar mutane fiye da 20,000 a Arewa Maso Gabashin Kasar nan.

Haka kuma dai ya koka da yadda gazawar  ta mayarda mutane sama da miliyan biyu ‘yan gudun hijira da kuma yara marayu sama da 75,000.

Ya yi wa mutane tuni akan yadda wasu tsiraran mutane a gwamnatin bayan suka wawushe biliyoyin kudade da aka ware domin a yaki ‘yan tada kayar bayan.

 

A karshe ya yabawa sojojin game da namijin kokarin da suke yi wajen yakan ‘yan ta’addan da sadaukar da rai da suke yi ba dare ba ranan domin kasar ta zauna lafiya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like