
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham ya fi son shiga Real Madrid daga Borussia Dortmund, duk da sha’awar da ƙungiyoyin Liverpool da Manchester City da kuma Manchester United kan matashin mai shekara 19.
Benfica sun ce albarka ga tayin yuro miliyan 100 da wani kulob da ba a bayyana sunansa ba, ya yi kan ɗan wasan tsakiya na ƙasar Argentina Enzo Fernandez, wanda ake alaƙanta shi da Liverpool da kuma Real Madrid, sun dai ce ba za a sayar da ɗan ƙwallon mai shekara 21, ƙasa da yuro miliyan 120 ba, kamar yadda sharaɗin sakinsa ya tanada.
Real Madrid na da sha’awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Italiya mai shekara 24 Manuel Locatelli, wanda yake zaman aro a Juventus daga Sassuolo, idan ba su yi nasarar ɗaukar Bellingham ko Fernandez ba.
Chelsea ta amince da biyan yuro miliyan 12 kan kwanturagi da Molde don daukar ɗan wasan gaban Ivory Coast David Datro Fofana, mai shekara 20.
Golan Chelsea ɗan ƙasar Senegal Edouard Mendy, mai shekara 30, ya yi shakulacin ɓangaro da wani sabon kwanturagin shekara shida a Stamford Bridge saboda ya yi imani cewa kulob ɗin ba ya ganin cikakkiyar “darajarsa” wajen biyan albashi.
Babban jami’in kulob ɗin Shakhtar Donetsk Carlo Nicolini ya tabbatar cewa Arsenal na da sha’awar ɗaukar matashin ɗan wasan gaba na ƙasar Ukraine mai shekara 21, Mykhailo Mudryk.
Arsenal na ƙoƙarin ɗaukar dan wasan tsakiya na ƙasar Faransa mai shekara 27 Adrien Rabiot, wanda kwanturaginsa zai ƙare a Juventus da ƙarshen kaka.
Har yanzu Arsenal ba ta yanke shawara ba a kan ko za ta bar ɗan wasan baya na Portugal Cedric Soares ya tafi wani kulob ɗin a watan Janairu mai kamawa, ƙungiyar Fulham ce dai take jagorantar masu neman ɗan wasan mai shekara 31 wanda kuma yake jan hankalin Bayer Leverkusen da Villarreal.
Albashin da ake biyan Soares duk mako kimanin fam 75,000 shi ne ya zama ƙadangaren bakin tulu kan wannan lamari.
Crystal Palace na da sha’awar sake dauko ɗan wasan bayan Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 25, daga Manchester United, shekara uku bayan sayar da shi ga kulob ɗin na Old Trafford.
Nottingham Forest sun bi sahun Fulham a neman ɗan wasan tsakiya na ƙasar Mali mai shekara 29, Abdoulaye Doucoure daga Everton.
Leeds na gudanar da tuntuɓa kan ɗan wasan bayan Ingila mai shekara 26, da ke taka leda a Everton Mason Holgate, haka zalika su ma Lyon sun nuna sha’awa.
Babban kocin ƙungiyar Leeds Mark Jackson na tattaunawa da MK Dons game da buƙatar cike gurbin manajan kulob ɗin.
Liverpool da Manchester United na cikin ƙungiyoyin Firimiya Lig da ke sa ido kan ɗan wasan gaban Argentina mai shekara 16 da ke buga ƙwallo a Preston Felipe Rodriguez-Gentile, wanda ya ci ƙwallo biyar a wani wasa na Gasar cin Kofin Matasa ta FA.