Gotze ya koma Dortmund


Borussia Dortmund ta sake daukar tsohon dan wasanta Mario Gotze, kan yarjejeniyar shekara hudu, idan likitocin kungiyar sun kammala duba lafiyarsa.

Gotze mai shekara 24, ya buga wa Dortmund tamaula sau 83, kafin ya koma Bayern Munich da murza-leda a shekarar 2013.

Ya koma Munich ne kan yarjejeniyar kudi sama da fam miliyan 31, a matsayin wanda aka saya mafi tsada a lokacin a gasar Bundesliga ta Jamus.

Gotze ya taimaka wa Bayern ta lashe kofunan Bundesliga guda uku, shi ne kuma wanda ya ci wa Jamus kwallo a wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a 2014.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like