Guardiola ya nemi afuwar Gerrard bayan subul da baka



Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Pep Guardiola ya nemi afuwa ga Steven Gerrard kan kalaman da ya yi na zamewar tsohon kyaftin din Liverpool a wasa da Chelsea da ya fadi.

A lokacin da yake kare Manchester City kan tuhuma sama da 100 ta Financial Fair Play, ya kwatanta batun da tsautsayin da Liverpool ta yi rashin nasara 2-0 hannun Chelsea a 2013-14.

Dalilin da Liverpool ta kasa daukar Premier League, City ta lashe a lokacin.

”Ina neman afuwar Steven Gerrard kan kalaman da na yi da ba su da ce ba,” in ji Guardiola.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like