Guatemala Ta Fara Mayar Da Ofishin Jakadancinta Birnin Jerusalem A wani mataki na jaddada goyon baya ga Amurka, kasar Guatemala ta bayar da sanarwar dauke ofishin jakadancinta na Isra’ila daga birnin Tel Aviv zuwa sabon babban birnin kasar wato, birnin Jerusalem.

Da yake bayar d umarnin, Shugaban Kasar Guatemala, Jimmy Morales ya bayyana cewa akwai kasashen da za su bi wannan sahun wajen mayar da ofisoshin jakadancinsu zuwa birnin Jerusalem.

You may also like