
Asalin hoton, Getty Images
Mutum fiye da miliyan daya na cikin duhu a sassa daban-daban na kasashen Amurka da Canada sakamakon guguwa mai karfi da ta addabi yankunan kasashen biyu.
Guguwar mai hade da dusar kankara, ta lalata wurare da dama musamman turakun lantaki a yayin da mutane ke cikin dan karen sanyi.
Garuruwar ta sa garuruwa da dama a Canada da Amurka na cikin yanayi na shirin kota kwana sannan kuma ta kai har kan iyakar Amurka da Mexico.
Manyan filayen jiragen sama sun soke tashin jirage zuwa wurare da dama a yayin da guguwar ke kara karfi.
Izuwa ranar Juma’a mutane fiye da miliyan daya da dubu dari uku a Texas da Maine ba suda lantarki saboda guguwar ta lalata turakun wuta.
A Canada kuwa mutum fiye da dubu dari biyu da tamanin ne ke cikin duhu a lardunan Quebec da Ontario.