Guguwa ta Kashe Daruruwan Mutane a Wasu Sassa na Amurka


 

Mahaukaciyar guguwa mai gudun kimanin kilomita dari biyu da ashirin a cikin sa’a guda ta tafka ta’adi na rayuka da dukiyoyi a wasu sassa na Amurka.

Guguar wacce aka yi wa lakani da Matthew na keta yankuna yankuna ta na yin ta’adi a duk inda ta bari. A yammacin jiya Alhamis guguwar ta bi ta yammacin tsibirin Bahamas, kuma ana tsammmanin za ta kai Florida a safiyar yau Juma’a.

Rahotanni na nuna cewa wannan guguwar ita ce mafi muni tun bayan girgizar kasar da ya faru shekaru shida da suka wuce. Ta yi ta’adin amfanin gona, gidaje da rayukan mutane da dama da haryanzu ba’a kayyade adadinsu ba.

Jami’in majalisar dinkin duniya a Haiti Mourad Wahba ya ce ana bukatar agajin gaggawa a kasar.

Tuni dai shugaban Amurka Barack Obama ya saka dokar ta-baci a yankunan da bala’in ya afka da inda ake tsammanin guguwar za ta kai.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like