Guguwar Matthew ta doshi Amurka


 

 

 

Kimanin mutanen Amurka Miliyan daya da rabi ke cikin shirin kauracewa gidajensu a Jihar Florida kafin isowar mahaukaciyar Guguwar Matthew mai tafe da iska bayan ta ratso Bahamas daga Haiti da Cuba inda ta kashe mutane 27.

An yi hasashen guguwar za ta nufi Amurka, yankin kudu maso gabashi, al’amarin da ya sa mutanen yankunan ke cikin shirin ko-ta-kwana.

Jihohin da ke fuskantar barazanar guguwar sun hada da Florida da Georgia da kudu da arewacin Carolina. Tuni hukumomi a Jihohin suka soma kwashe mutanen yankunan kafin isowar Guguwar.

Shugaban Amurka Barrack Obama ya yi kira ga mutanen yankin su bi umurnin hukumominsu domin kaucewa samun hasarar rayuka.

Shugaba Obama ya ce ya kamata mutanen yankunan su dauki duk wani gargadi da muhimmaci da hukumomin yankunansu suka bayar musamman idan an ce su kauracewa gidajensu.

Guguwar ta ratso zuwa yankin arewa maso gabashin Bahamas bayan ta yi barna a Haiti da Cuba da Jamhuriyyar Dominican.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like