Guguwar Matthew ta kashe daruruwan mutane a Haiti


 

 

Jami’an ceto a kasar Haiti sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon guguwar Matthew sun karu zuwa sama da 400. Yanzu haka kuma guguwar ta shiga Jihar Florida da ke Amurka cikin gudun kilomita kusan 200 a sa’a guda.

Gwamnatin Amurka ta kafa dokar ta-baci a Jihohin Georgia da Florida.

Rahotanni sun ce guguwar ta kashe mutane 50 a kudancin Roche-a-Bateau, bayan ta rusa gidaje da itatuwa da turakan lantarki.

Hukumomi sun ce akasarin inda aka samu mutuwar sun fito ne daga mutanen da ke zama a kauyuka da biranen da ke bakin teku, wadanda itatuwa ko turaku suka fadi a kan su.

Ofishin Jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutane 350,000 yanzu haka ke bukatar agaji a kasar.

Yanzu haka Amurka ta bukaci mutane sama da miliyan 3 su kauracewa gidajensu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like