Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa akan samar da takin zamani da Gas, a safiyar yau tare da tawagar Gwamnatin Tarayya suka bar Nijeriya zuwa kasar Morocco domin sanya hannu a wata yarjejeniya da Gwamnati kasar ta Morocco akan samar da bututun iskar gas daga Nijeriya da musayar samar da taki daga Kasar Morocco.
Sauran yan tawagar sun hada da Gwamnan Jihar Ebonyi, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ministan Noma, Karamin Ministan Cinikayya da Zuba Jari, da kuma Shugaban Kamfanin Mai na Kasa.