Gwamna Badaru na jihar Jigawa ya bar Nijeriya zuwa Ƙasar ta Belgium ne a jiya ta Jirgin Egypt Air tare da manajin darektan hukumar noma da raya karkara na jihar Jigawa (JARDA), kuma shine kaɗai Gwamnan da aka zaɓa domin ya wakilci Gwamnoni 19 na Arewacin Nijeriya a taron.
A yayin taron Gwamnan zai gabatar da jawabi, ya kuma gana da waɗanda suka shirya taron, masu zuba jari da kungiyoyi masu bada basussuka na harkar noma, da zimmar janyo ra’ayin masu zuba jari domin zuwa jihar Jigawa da samar da basussuka mara ruwa ga manoman jihar Jigawa.
Wasu suna ganin hakan ba ƙaramin karamci ba ne ga Gwamna Badaru da kuma ɗaukacin al’umar jihar Jigawa na kasancewar Gwamnansu shine ɗaya tilo da aka zaɓa domin wakiltar sauran Gwamnonin jihohin Arewacin kasar nan.