Gwamna Bagudu Na Kebbi Ya Rusa Majalisar Zartarwar Jihar
Gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da rusa majalisar zartarwar jihar.

Wannan mataki zai fara aiki ne daga Laraba 7 ga watan Satumbar 2022 a cewar wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri ya fitar.

“Mai girma Gwamna na mika godiyarsa ga dukkan mambobin majalisar da aka rusa saboda irin gudunmowa da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma ciyar da jihar gaba.” In ji Yauri.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin rusa majalisar zartarwar ba, amma ta ce nan ba da jimawa ba za a sake kafa wata majalisar.

“Nan ba da jimawa ba, za a sake kafa wata majalisar zartarwar, wacce za ta kunshi wasu daga cikin mambobin majalisar da aka rusa da kuma wasu da ba sa ciki.” Yauri ya ce.

You may also like