GWAMNA DAKWAMBO YA KOKA DA KARANCIN MAN FETUR



Gwamnan jihar Gwambe Alhaji Ibrahim Dankwambo ya bayyana rashin jin dadin sa da halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki na karancin man fetur, abin da ya haifar da hauhawar farashin abubuwan bukatun rayuwa. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta shafin sa na facebook, inda ya bayyana cewa, ba zai yiwu bayan karin kudin da gwamnati ta yi na kudin man fetur daga naira 85 zuwa 145 lokaci guda, amma kuma har yanzu Nijeriya ba ta yi sallama da wannan wahala ba. 

Ya nemi dukkan masu ruwa da tsaki a wannan harka ta samar da man fetur su tabbatar da an kawo karshen dogayen layukan mai, domin ‘yan Nijeriya musamman Kirista su samu damar gudanar da bukin Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin sauki. 

You may also like