Gwamna El-Rufa’i Ya Jinjina Wa Yunkurin Samar Da Zaman Lafiya Tsakanin Addinai


elrufai

 

Ranar Jumu’a 19 ga watan Agusta 2016 ta kasance muhimmiyar ranar da ta shiga cikin kundin tarihin yunkurin inganta hulda a tsakanin mabiya addinai a Kaduna. Inda a wannan ranar, muhimman mutane sun hadu a Kaduna domin kaddamar da cibiyar kasa da kasa ta samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin addinai. Cibiyar ta samu goyon bayan Majalisar Coci-Coci ta Duniya da Cibiyar Musulunci ta Ahal Al-Bayt.

Cibiyar ta ‘Tabbatar da Zaman Lafiya da Fahimtar Juna a Tsakanin Addinai,’ wacce ke a kan titin Jabi a cikin kwaryar Kaduna ta karbi bakuncin nagartattun Shugabanni, wadanda ke fadi-tashin samar da zaman lafiya a Nijeriya. Shugabanni kamar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Shugaban Cocin Katolika na Abuja, John Cardinal Onaiyekan, da Shugaban Majalisar Kiristoci ta Nijeriya, Emmanuel Udophia, da Sakataren Majalisar Yusuf Ibrahim Wushishi.

Sauran su ne: Sakatare-Janar na Jama’atu Nasril Islam, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, da Rabaran Israel Akanji, wanda ya wakilci Shugaban kungiyar Kiristoci ta Nijeriya, da Rabaran Samson Ayokunle, da Dakta Usman Bugaje da Injiniya Samuel Salihu Tsohon Sakatare-Janar na kungiyar CAN, da Rabaran Joseph Hayab, Kakakin kungiyar Kiristoci reshen Arewa, da sauran Shugabannin addini.

Amfanin assasa cibiyar a Kaduna, shi ne saboda jihar tana cikin muhimman wuraren da rikice-rikicen addini da fadace-fadacen kabilanci suka gudana tun a shekarun 1980’s. Cibiyar na da manufar tattara bayanan dangantakar dukkanin addinai domin tabbatar da tsare-tsare da ci-gaban kasa. Haka ma cibiyar za ta yi yaki, tare da neman goyon bayan hana amfani da addini domin biyan bukatar wasu ta siyasa, wanda hakan ya jefa kasar nan cikin kashe-kashe marar iyaka.

Gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana cewa,

“Aikina a yau abu ne mai sauki, wato kaddamar da wannan muhimmiyar cibiya. Abu na biyu shi ne, gode wa Majalisar Coci-coci ta dDuniya da Cibiyar Musulunci ta Ahal Al-Bayt a bisa ga zaben Kaduna a matsayin mazaunin wannan cibiya. Muna godiya kwarai, kuma ba mu dauki wannan karramawa a matsayin karama ba, domin za a iya yin wannan cibiya a ko’ina, amma kuma bisa ga hikima kuka zabi kafata a Kaduna. Muna godiya kwarai.”

Da yake bayyana muhimmancin cibiyar, Gwamna el-Rufa’i ya bayyana wa muhimman bakin kadan daga cikin tarihin birnin Kaduna da cewa, “Kaduna matashin birni ne, domin da yardar Allah a watan Yuli na shekara mai zuwa za mu yi bukin cika shekaru 100 da kafuwar Kaduna. Birni ne da ke da muhimmin tarihi, hasali ma shi kadai ne birnin da aka tsara a Nijeriya, domin Luggard ya sanya hannu a dokar tsare-tsaren birni a Yuli 1917. Nan kadai ne birni a Nijeriya da kowane dan Nijeriya da kuma wanda ba dan Nijeriya ba zai kira a matsayin nasu, ba tare da fargabar nuna bambancin addini ko kabila ba.”

A wani bangare marar dadi na labarin Gwamnan, ya ci gaba da bayyana cewa,

“Sai dai kash! Tun daga 1980 Kaduna ta samu kanta cikin rikice-rikice har 12, wadanda aka alakanta da kabilanci da kuma addini, wanda ya zama sanadiyyar kashe mutane dubu 20, tare da asarar kaddarori na Bilyoyin Naira. Abin bai tsaya a nan ba, mutanenmu sun rarrabu, haka ma birnin Kaduna ya rarrabu har zuwa kogin Kaduna. Mafi yawan Kiristoci suna zaune ne a gefen Kudancin kogin, sannan mafi yawan Musulmi suna zaune a gefen Arewacin kogin. Wannan shi ne abin da muka gada, wannan ba ita ce Kadunar da na taso ba. Wannan ne dalilin da ya sa wannan cibiyar take da muhimmanci garemu, wanda alama ce da ke nuna cewa za mu hada kan mutanenmu.”

Da yake bayyana fatarsa ga wannan yunkurin, Gwamnan cewa ya yi, “gwamnatin Jihar Kaduna ba wai kawai ta yaba da samar da wannan cibiyar ba kawai, a’a, haka ma za mu bayar da dukkan goyon bayanmu domin ganin an samu nasara. A tsare-tsaren gwamnati ,muna nuna rashin goyon baya ga wadannan bambance- bambance. Misali, mun gano cewa gwamnati tana da sashe biyu na addinin Musulunci da lamurran Kirista, dukkaninsu mun rusa su, muka mayar da su daya domin mun yarda cewa wadannan addinan biyu bambancin da suke da shi kadan ne, kuma hakkinmu ne mu sanya su yin aiki tare domin su fahimci juna.”

A nasa jawabin Sarkin Musulmi ya bayyana cewa kaddamar da cibiyar, wani sako ne ga al’ummomin duniya a kan rashin bayyanar da gaskiyar lamari da ake yi wa addini. “Wannan dama ce a garemu domin mu bayyana wa duniya baki daya cewa muna da namu kananan matsaloli a Nijeriya kamar ko wane sashe na duniya, amma ba fada ko kashe-kashe muke yi ba. Zama daya a matsayin Musulmi da Kirista domin a fahimci juna, tare da tsayawa a kan koyarwar littafanmu abu ne mai muhimmanci wanda zai nuna wa al’umma cewa mun yarda da abin da muke fada kuma za mu ci gaba da koyarwa a kan zaman lafiya. Wannan cibiya ce ta zaman lafiya da fahimtar juna, duk wani wanda ke da matsala komai girmanta, idan aka gabatar da ita a wuraren da ya dace aka zauna aka tattauna, to za a samu mafita. Daukar makamai, tare da furta zafafan kalaman da ke iya haddasa rikici, ba zai amfane mu ba ko kadan.”

Sarkin Musulmin, wanda ya bayyana muhimmancin tattaunawa domin samun maslaha, ya rufe da cewa, “ina ganin abu mafi muhimmanci da ya kamata mu yi wa addinanmu da al’ummarmu shi ne, samar da hanyar da za su yi aiki daya domin su tattauna. Na yarda tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa a duk wani lamari mai wuyar sha’ani, ba wai amfani da karfi ba. Mun ga kasashen da aka yi amfani da karfi da makamai, amma kuma ba su samu zaman lafiya ba. Mun ga duniyar da mutane ke kashe ‘yan uwansu, amma kuma ba a samu zaman lafiya ba. Mutane suna yaki domin su tabbatar da wani tsari da suke ganin shi ne ingantacce, amma kuma har wayau babu zaman lafiya.”

“Shin za mu bayyana cewa idan Musulmi yana kashe Musulmi, babu wata matsala? Shin bai kamata mu hadu domin mu taimaki al’ummarmu ba? Ko kuwa za mu ce babu wata matsala idan Kirista ya kashe dan uwansa Kirista? Wannan ba shi ne koyarwar littafanmu ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa nake ganin wannan cibiyar ta bambanta da saura, saboda muna son ta zama cibiyar da mutane za su zo su samu bayanan abubuwan da ke faruwa. Idan mutane suka samu wata matsala, wanda abu ne da ke faruwa, ina rokon a je wannan cibiyar domin warware matsalolin da ake fama. A dauki lamarin da matukar muhimmanci ko a matakin Tarayya ko Jiha a ga yadda za mu samar da zaman lafiya ga dukkanin al’ummarmu.”

Sakatare- Janar na Kungiyar Taron Kara wa Juna Sani na Coci, Rabaran Dakta Olab Fykse Tbeit, wanda ya bayyana gamsuwa kan ingancin aikin cibiyar, ya yi bayanin cewa, “da farko muna son a dauki cibiyar a matsayin ta dukkanin addinai, wacce kowa da kowa zai kalla a matsayin mallakin Musulmi da Kirista ba tare da kowane irin bambanci ba. An tsara Hukumar Gudanarwa tsakanin Shugabannin Musulmi da Kirista kashi 50/50, kuma manufar ita ce ma’aikatan cibiyar za su yi aiki na kwararru, kazalika za su wakilci addinan biyu. Abu na biyu shi ne, kungiyar Majalisar Kirista ta Nijeriya da Jama’atu Nasril Islam za su kasance gaba wajen tafiyar da cibiyar. Duniya tana kallonku a yanzu domin ganin aikin da kuke yi a Kaduna wanda zai iya magance tashin hankali a ko’ina a duniya.”

“A bisa ga abin da na ji daga gare ku a yau, ina da tabbacin za su zama alama ko manuniyar samun nasara a duniya. Zan kammala wannan jawabin tare da bayyana godiya kan sadaukar da kai da jajircewar gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasir el-Rufa’i kan yadda yake aikin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin addinai a Kaduna.”

You may also like