Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i ya maka dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani kotu inda ya nemi ya biya shi diyyar Naira Bilyan biyu bisa zargin kiransa mashayin giya kuma mutumin da ya kunyata Shugaba Buhari.
El Rufa’i ya nemi kotun ta bayyana ikirarin dan majalisar a matsayin marasa Kanshin gaskiya. Sai dai kuma Sanata Shehu Sani ya musanta wannan kazafi da El Rufa’i ya yi masa inda ya jaddada cewa a shirye yake su hadu da Gwaman a kotu.