Gwamna El-Rufa’i Zai Fuskanci Babban Kaluble A Zaben Cikin Gida Na Jam’iyyar APCGwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i zai fuskanci barazana tare da kalubale mai tsanani a zaben fidda gwani na zabe mai zuwa a 2019, bisa ga la’akari ga mamya manyan kungiyoyi masu tarin yawa a jihar ta Kaduna da suke ta kira ga Rt Hon Aminu Abdulfatah da ya fito takarar Gwamnan Kaduna, wato tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar Kaduna. Wanda kuma alamu duk sun nuna Hon Aminu Abdulfatah zai iys amsa wannan kira na al’ummar jihar ta Kaduna.

 Masana Harkokin siyasa na ganin za’a fafata kwarai tsakanin gwamna El rufai da Aminu Abdulfatah a wajen zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki bisa Ga La’akari da kuma sakamakon nasarori da aketa samu na fahimtar juna tsakanin kungiyoyi da (Delegates) na jam’iyyar APC a kadunan 

Bugu da kari kuma (Delegates) da kungiyoyin samari sun samu nutsuwa akan Hon. Aminu Abdulfatah din Dalili kuwa Shine Shidai Hon Aminu Abdulfatah dan siyasa ne mai adalci da gaskiya, hakane ma yasa Tun Farkoma Aka Faro Tafiyar Shugaba Buhari dashi 

Hakika jajirtaccen tsohon dan siyasa ne sananne kuma a jihar ta Kaduna Ya jima Ana gwagwarmaya dashi a fagen siyasa kuma duk Wanda suka sanshi sun sanshi da gaskiya da adalci a wajan jagorancin Al’umma, saboda yana daya daga cikin wadanda suka jawo shugaban kasa muhammad Buhari zuwa fagen siyasa tun farkon shigar shi siyasa a 2002, wato (Buhari think tank group) 

Kadan daga cikin ‘yan kungiyar da suka faro tafiyar ta Buhari sune suka hada da su 
1Malam Mamman Daura,
2 Malam Adamu Adamu,
3 Malam Salihu Abubakar,
4 prof Abdullahi Mustapha
5 da Malam Bello Damagum,
6 Bala Muhammad 

Dadai sauran wadanda suka bada gudunmawa a harkar 

Samari da al’ummar jihar Kaduna sun ga babu wanda ya dace su marawa baya a zaben 2019 kamar Hon Aminu Abdulfatah, Saboda zai kula da Al’umma ta jihar ta kaduna, zai kula da kowa da kowa, kuma zai kai jam’iyyar APC ga cin nasara a zaben gwamna mai zuwa na 2019 a jihar Kaduna. Bisa ga tabbacin da binciken Kungiyoyin samari da matasan jahar sunyi la’akari da yadda abubuwa ke gudana a jihar kaduna, sunga Hon Aminu Abdulfatah shine da yardar Allah tareda gudummuwar samari da matasa da tsofaffi mata da maza zai ceto jam’iyyar tasu ta APC a jihar kaduna Daga Halinda ta Tsinci kanta 

Bugu da kari Hon Aminu Abdulfatah zai dawo da martabar jam’iyyar APC a Kaduna saboda kwarewa da sanin makaman siyasa da jajircewa da yake da shi, idsn ya hau karagar mulkin jihar Kaduna.

Masana siyasa sun kara da cewa Hon Aminu Abdulfatah dan siyasa ne mai akida, siyasa ta akida yakeyi, yayi kakakin majalisar dokoki ta Wannan jihar munga yadda ya tafiyar da Al’umma yadda yake sauraron talakawa yake baiwa kowa hakkin shi, bisa la’akari da haka al’umma suka ga shine ya cancanta ya jagoranci jihar kaduna a 2019. 

Daga yanzu babu sauran a baiwa (Delegates) kudi su zabi dan takara da ba zai taimakawa al’umma ba, dole (Delegates) su zabi wanda al’umma ke so don tsayawa takara a jam’iyyar APC. Yanzu lokaci ne da baza’a kara yadda jam’iyyar APC ta tsaida dan takara mara inganci ba. A karshe Muna kira ga Al’ummar jihar kaduna daga matakin Gunduma (Ward) har zuwa matakin kasa baki daya da jama’a su rinka tunatar da (Delegates) masu wakiltar (Ward) din su da cewa wanda sukeso shi za’a zaba a matsayin dan takara a jam’iyyar APC.

Kira daga Kungiyar Matasan jahar Kaduna Masu Kishin Jahar Kaduna baki daya. Dogaro Da nazari da dogon tunani akan abinda zai zama Mafita Ga Al’ummar Jahar Kaduna yasa Mukayi wannan kira.

You may also like