Gwamna Ganduje Ya Cire Jar Hula


Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda, a yayin da rahotanni suka bayyana cewa ya cire jar hular da ya dade yana sanyawa wacce take alamta biyayya ga akidar Siyasa ta Kwankwasiyya. 


Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya cire jar hular ne a inda ya gabatar da jawabi a gaban dubban jama’a a jihar Jigawa, yayin bikin karbar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa maso yammacin Najeriya, Sanata Danladi Abdullahi Sankara wanda ya canza sheqa zuwa Jam’iyyar APC.
Gwamna Ganduje ya kasance bai taba cire jar hularsa ba a bainar jama’a, tun a lokacin da tsohon gwamnan Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da taken tafiyarsa a siyasance da “Kwankwasiyya”, tare da yin amfani da jajayen huluna a matsayin alama ga magoya bayan tafiyar.
Duk da cewa an samu rashin jituwa a baya a tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Ganduje, lamarin da ya saka wadansu ‘yan siyasa magoya bayan Ganduje suka tube jajayen hulunansu, amma duk da haka Ganduje bai taba fitowa bainar jama’a ba tare da yana sanye da jar hula ba matuqar har idan ya na sanye da manyan riguna (babbar riga ko dogayen kaya).

You may also like