Gwamna Ganduje Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na Jihar Kano


Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na Mako Mako wanda ake Gabatarwa a Fadar Gwamnatin Kano.

A Jawabinsa Gwamna Ya fara da Taya Al’ummar Jihar Kano da Majalisar Zartarwa Murnar cikar Nijeriya Shekara 57 da Samun ‘Yancin Kai daga Turawa.

Daga bisani Gwamnan Ya bayyana Rasuwar AVM Mukhtar Muhammad a Matsayin Babban Rashi tare da Tijjani Ado Ahmad wanda aka yi Addu’a ta Musamman domin Allah Ya Jikansu da Rahma.

You may also like