Gwamna Ganduje Ya ‘YanTa Fursunoni 50 A Bikin Cikar Jihar Kano Shekaru 50 Da Kafuwa
A yau rana ta biyu domin murnar cikar jihar Kano Shekaru Hamsin Da kafuwa gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci gidan kurkuku dake Kurmawa domin ya gana da daurarru yayin ganawarsa da fursunonin yayin alkawarin kawo musu na’ura mai kwakwalwa domin sun bayyana cewa ana koya musu ilimi fanni daban daban a ciki. 

Gwamna Ganduje ya ce ba zai yiwu yazo gidan kurkuku yafita haka ba, nan take yabada umarnin yanta bursunoni 50 masu kananan laifuka kama da marasa lafiya ko tsofaffi kokuma wanda akayimusu tara ta kudi kankani suka kasa biya. 

Daga karshe gwamna Ganduje yayi kira  da ‘yantantun dasu zama jakadu nagari da zarar sun fito daga gidan kurkukun. 

Gwamna Ganduje yana tare da rakiyar, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas, tsohon mataimakin Gwamna Abdullahi Gwarzo, tsohuwar Kwamishinyar Noma Kuma Tsohuwa maibawa shugaban kasa shawara akan harkokin noma Hajiya Dr Baraka Sani, shugaban shugabanin kananan hukumomi Algon Hon Muktar Ishaq Yakasai da kwamishinan Maikatar Aiyuka da Gidaje Hon Shehu Haruna Lambu. Hon Ali Baba Agama Lafiya maibawa Gwamna Shawara Akan Addinai tare da Sauran manyan baki. 

You may also like