Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana kudirin gwamnatinsa na tallafawa masu farautar naman kwadi a jahar Kano.
A wani shawagi da ya kai garin Kadawa, inda ya gana da wasu manoman shinkafa, rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya bayyana cewa gwamnan ya hadu da wasu mutane da ke kama kwadi da suka yada zango akan hanyar ta Kadawa.
Yawancinsu bakin haure ne daga jahohin Oyo, Benue, Ondo da kuma inyamirai. Su na farautar kwadin ne sannan su bankare, su gasa, su kuma sayar a fadin kasar nan.
Jaridar ta gana da daya daga cikin masu kamun kwadin mai suna Hajiya Sidi Kada ‘yar asalin jahar Oyo wacce ta ce ta shafe tsahon shekaru 15 ta na wannan sana’a kuma ta na matukar samun kudi. A fadarta, a rana daya ta kan yi cinikin N10,000.
Ta kara da cewa ana sayarda kowanne kwado daya akan N70 zuwa N80, yayin da matattu ke tafiya akan N4 kowanne daya.
Gwamna Ganduja ya tabbatarwa da masu farautar kwadin cewa gwamnatinsa za ta tallafawa sana’ar tasu da injin busar da kwadin cikin sauki.